Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ciwon Hezekiya da Warkewarsa

1. A waɗannan kwanaki sai Hezekiya ya yi rashin lafiya har yana gab da mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya zo wurinsa, ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka, gama mutuwa za ka yi, ba za ka warke ba.”

2. Hezekiya kuwa ya juya fuskarsa bango, ya yi roƙo ga Ubangiji, yana cewa,

3. “Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.

4. Kafin Ishaya ya fita daga filin tsakiyar fādar, sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce,

5. “Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama'ata cewa, ‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Ubangiji.

6. Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuwa cece ka, kai da wannan birni daga hannun Sarkin Assuriya, zan tsare wannan birni don kaina da kuma don bawana, Dawuda.’ ”

7. Sai Ishaya ya ce, “Ku yi masa farsa da ɓaure, marurun zai warke.”

8. Hezekiya kuwa ya ce wa Ishaya, “Mece ce alama, cewa Ubangiji zai warkar da ni har in haura zuwa Haikalin Ubangiji a rana ta uku?”

9. Sai Ishaya ya ce, “Wannan ita ce alama daga wurin Ubangiji, Ubangiji zai cika alkawarin da ya yi. Ƙaƙa kake so, inuwa ta yi gaba da taki goma, ko kuwa ta yi baya da taki goma?”

10. Hezekiya ya amsa, ya ce, “Ai, ya fi sauƙi inuwa ta yi gaba da taki goma da ta yi baya da taki goma.”

11. Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya komar da inuwa baya da taki goma, bayan da ta riga ta wuce a matakin sarki Ahaz.

Hezekiya ya Karɓi Manzanni daga Babila

12. A lokacin nan sai Merodak-baladan, ɗan Baladan, Sarkin Babila, ya ji labarin rashin lafiyar Hezekiya, sai ya aiki manzanni da wasiƙa da kyautai su kai wa Hezekiya,

13. Hezekiya kuwa ya marabce su, ya kuma nuna musu dukan taskokin dukiyarsa na azurfa, da na zinariya, da na turare, da na mai mai daraja, da na makaman yaƙinsa, da dukan abin da yake akwai a cikin ɗakunan ajiyarsa. Ba abin da ya rage daga cikin gidansa, ko a mulkinsa wanda bai nuna musu ba.

14. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin sarki Hezekiya ya ce masa, “Daga ina ne waɗannan mutane? Me suka ce maka?”Hezekiya ya amsa, ya ce, “Sun zo daga ƙasa mai nisa, wato Babila.”

15. Ishaya ya ce, “Me suka gani a fādarka?”Hezekiya ya ce, “Sun ga duk abin da yake ciki, ba wani abu kuma daga cikin taskokina da ban nuna musu ba.”

16. Sa'an nan Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji abin da Ubangiji ya ce,

17. ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe duk abin da yake cikin gidanka, da abin da kakanninka suka tanada, zuwa Babila.

18. Za a kuma kwashe waɗansu 'ya'yanka da ka haifa zuwa Babila, can za a maishe su babani a fādar Sarkin Babila.’ ”

19. Sarki Hezekiya kuwa ya fahimci za a yi zaman lafiya da salama a zamaninsa, don haka ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”

Rasuwar Hezekiya

20. Sauran ayyukan Hezekiya da dukan ƙarfinsa, da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa don ya kawo ruwa cikin birnin, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

21. Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.