Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 18:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.

13. A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su.

14. Sai Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya aika zuwa wurin Sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka ƙyale ni, duk abin da ka ɗora mini zan ɗauka.” Sai Sarkin Assuriya ya ce wa Hezekiya Sarkin Yahuza ya ba shi talanti ɗari uku na azurfa, da talanti talatin na zinariya.

15. Hezekiya kuwa ya ba shi dukan azurfar da take cikin Haikalin Ubangiji, da wanda yake cikin baitulmali na gidan sarki.

16. A lokacin sai Hezekiya ya kankare zinariyar da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin Haikalin Ubangiji da ita, ya ba Sarkin Assuriya.

17. Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki.

18. Sa'ad da suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka fito.

19. Sa'an nan Rabshake ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya, cewa mai girma, Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ga wa kake dogara?

20. Kana tsammani maganganu kurum su ne dabara da ƙarfin yin yaƙi? To, ga wa ka dogara har da ka tayar mini?

21. Ga shi yanzu, kana dogara ga Masar, wannan karyayyen sandan kyauro, wanda yakan yi wa hannun mutumin da yake tokarawa da shi sartse. Haka Fir'auna Sarkin Masar, yake ga dukan waɗanda suke dogara gare shi.’

22. “Amma idan ka ce mini, ‘Ina dogara ga Ubangiji Allahnmu,’ to, ba masujadansa na kan tuddai da bagadansa ne Hezekiya ya rurrushe ba? Yana ce wa mutanen Yahuza da Urushalima, ‘Za ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima?’

23. Sai ka zo, ku daidaita da ubangidana, Sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu (2,000), idan za ka iya samun mahayansu.

24. Ba ka isa ka kara da ko mafi ƙanƙanta na shugabannin sojojin maigidana ba, amma har kana dogara ga Masar don samun karusai da mahaya?

25. Kana tsammani, ba da yardar Ubangiji ba ne na kawo wa wurin nan yaƙi don a hallaka shi? Gama Ubangiji ya ce mini, ‘Ka kai wa wannan ƙasa yaƙi don ka hallaka ta.’ ”

Karanta cikakken babi 2 Sar 18