Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 17:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Wannan abu ya sami Isra'ila saboda sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fito da su daga ƙasar Masar, daga hannun Fir'auna, Sarkin Masar. Suka bauta wa gumaka.

8. Suka bi al'adun al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora a gabansu, da al'adun da sarakunan Isra'ila suka kawo.

9. Jama'ar Isra'ila kuma suka yi wa Ubangiji Allahnsu abubuwan da ba daidai ba, daga ɓoye. Sun gina wa kansu matsafai a dukan garuruwansu daga hasumiya zuwa birni mai garu.

10. Suka kuma kafa wa kansu ginshiƙai da siffofin gumakan Ashtarot a kowane tudu da a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.

11. Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.

12. Suka bauta wa gumaka waɗanda Ubangiji ya ce musu kada su bauta musu.

13. Amma Ubangiji ya faɗakar da jama'ar Isra'ila da jama'ar Yahuza ta bakin annabawa da kowane maigani, cewa su bar mugayen hanyoyinsu, su kiyaye umarnansa da dukan dokokinsa waɗanda ya umarci kakanninsu da su, waɗanda kuma ya aiko musu ta wurin bayinsa annabawa.

14. Duk da haka suka ƙi kasa kunne, suka taurare zuciyarsu kamar yadda kakanninsu suka yi, waɗanda ba su yi imani da Ubangiji Allahnsu ba.

15. Suka yi watsi da dokokinsa, da alkawarinsa da ya yi wa kakanninsu, da kuma faɗakarwar da ya yi musu. Suka bi gumakan banza, suka zama banza, suka bi halin al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda Ubangiji ya umarce su kada su yi kamarsu.

16. Suka bar dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu siffofin zubi na 'yan maruƙa biyu, suka yi gunkiyan nan, Ashtoret, suka yi wa taurari sujada, suka bauta wa Ba'al.

Karanta cikakken babi 2 Sar 17