Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 17:27-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Sa'an nan Sarkin Assuriya ya umarta a aiki firist ɗaya daga cikin firistocin da aka kwashe daga can, ya tafi, ya zauna can domin ya koya musu shari'ar Allahn ƙasar.

28. Sai firist ɗaya daga cikin firistocin da suka kwashe daga Samariya, ya zo, ya zauna a Betel. Shi kuwa ya koya musu yadda za su yi tsoron Ubangiji.

29. Amma duk da haka kowace al'umma ta riƙa yin gumakanta, tana ajiye su a wuraren yin tsafin na kan tuddai waɗanda Samariyawa suka gina. Kowace al'umma kuma ta yi haka a garin da ta zauna.

30. Mutanen Babila suka yi Sukkot-benot, mutanen Kuta suka yi Nergal, mutanen Hamat suka yi Ashima.

31. Awwiyawa suka yi Nibhaz da Tartak, mutanen Sefarwayim suka miƙa 'ya'yansu hadaya ta ƙonawa ga Adrammelek da Anammelek, gumakansu.

32. Su ma suka yi tsoron Ubangiji, suka sa mutane iri dabam dabam su zama firistocin wuraren tsafinsu na kan tuddai. Firistocin nan suka miƙa hadayu dominsu a ɗakunan tsafinsu na kan tuddai.

33. Waɗannan mutane su ma suka yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka bauta wa gumakansu ta hanyar da al'umman da aka kwaso su daga cikinsu suke yi.

34. Har wa yau suna yin yadda suka yi a dā. Ba su yi tsoron Ubangiji ba, ba su bi dokoki, ko ka'idodi, ko shari'a, ko umarnan Ubangiji ba, waɗanda ya umarci 'ya'yan Yakubu, wanda ya sa wa suna Isra'ila.

35. Ubangiji ya yi alkawari da 'ya'yan Yakubu, ya kuma umarce su kada su yi wa gumaka sujada ko su durƙusa musu, ko su bauta musu, ko su miƙa musu hadayu.

36. Amma su yi tsoron Ubangiji, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar da iko mai girma da ƙarfi, shi za su yi wa sujada, shi kuma za su miƙa wa hadayu.

37. Sai su yi biyayya da dokokinsa da umarnansa da ya rubuta musu. Kada su ji tsoron waɗansu alloli.

Karanta cikakken babi 2 Sar 17