Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 1:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Manzannin kuwa suka koma wurin sarki. Sarki ya ce, “Me ya sa kuka komo?”

6. Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, ‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra'ila, har aka aike ku ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”

7. Sarki ya tambaye su, “Yaya mutumin yake, shi wanda ya sadu da ku, ya faɗa muku irin wannan magana?”

8. Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.”Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”

9. Sa'an nan sarki ya aiki shugaba tare da mutum hamsin su taho da Iliya. Mutumin kuwa ya haura wurin Iliya a kan dutse, ya ce masa, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko.”

10. Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.

11. Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba tare da mutum hamsin. Suka tafi, shugaban ya ce wa Iliya, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko da sauri.”

Karanta cikakken babi 2 Sar 1