Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 1:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan rasuwar Ahab, Sarkin Isra'ila, sai Mowabawa suka tayar wa Isra'ilawa.

2. Ahaziya ya faɗo daga tagar benensa a Samariya, ya kuwa ji ciwo ƙwarai. Sai ya aiki manzanni, ya ce musu, “Ku tafi, ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron, ko zan warke daga wannan ciwo.”

3. Sai mala'ikan Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe, ya ce, “Tashi, ka tafi, ka sadu da manzannin Sarkin Samariya, ka ce musu, ‘Ba Allah a Isra'ila da za ku tafi ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron?’

4. Ku faɗa wa sarki, Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi.

5. Manzannin kuwa suka koma wurin sarki. Sarki ya ce, “Me ya sa kuka komo?”

6. Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, ‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra'ila, har aka aike ku ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”

7. Sarki ya tambaye su, “Yaya mutumin yake, shi wanda ya sadu da ku, ya faɗa muku irin wannan magana?”

8. Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.”Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”

9. Sa'an nan sarki ya aiki shugaba tare da mutum hamsin su taho da Iliya. Mutumin kuwa ya haura wurin Iliya a kan dutse, ya ce masa, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko.”

10. Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.

Karanta cikakken babi 2 Sar 1