Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 5:20-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai Dawuda ya zo Ba'al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.”

21. Filistiyawa suka gudu, suka bar gumakansu a nan, Dawuda da mutanensa suka kwashe su.

22. Filistiyawa suka sāke haurawa, suka bazu a kwarin Refayawa.

23. Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.

24. Sa'ad da ka ji motsin rausayawar rassan itatuwan doka, sai ka yi maza, ka faɗa musu, gama Ubangiji zai wuce gaba domin ya bugi rundunar Filistiyawa.”

25. Sai Dawuda ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya yi ta bugun Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.

Karanta cikakken babi 2 Sam 5