Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 5:10-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Dawuda kuwa ya ƙasaita, gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana tare da shi.

11. Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al'ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida.

12. Dawuda kuwa ya gane lalle Ubangiji ya tabbatar da shi sarki bisa jama'ar Isra'ila, ya kuma ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa, Isra'ila.

13. Bayan zuwan Dawuda Urushalima daga Hebron, sai ya ɗauki waɗansu ƙwaraƙwarai, ya kuma auri waɗansu mata. Aka kuma haifa masa waɗansu 'ya'ya mata da maza.

14. Sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima ke nan, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,

15. da Ibhar, da Elishuwa, da Nefeg, da Yafiya,

16. da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.

17. Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila, sai dukansu suka haura zuwa neman ran Dawuda. Da Dawuda ya ji Filistiyawa suna nemansa, sai ya gangara zuwa kagara.

18. Filistiyawa kuwa suka zo suka bazu a kwarin Refayawa.

19. Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”

20. Sai Dawuda ya zo Ba'al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.”

21. Filistiyawa suka gudu, suka bar gumakansu a nan, Dawuda da mutanensa suka kwashe su.

22. Filistiyawa suka sāke haurawa, suka bazu a kwarin Refayawa.

23. Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.

24. Sa'ad da ka ji motsin rausayawar rassan itatuwan doka, sai ka yi maza, ka faɗa musu, gama Ubangiji zai wuce gaba domin ya bugi rundunar Filistiyawa.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 5