Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 23:8-24-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ga sunayen jarumawan Dawuda, Yosheb-basshebet, daga Takemon, shi ne ɗaya daga cikin shugabanni uku. Ya girgiza māshinsa, ya kashe mutum ɗari takwas baki ɗaya.

9. Wanda yake biye da shi a cikin su uku ɗin shi ne Ele'azara, ɗan Dodo, ɗan Ahowa. Yana tare da Dawuda sa'ad da suka raina Filistiyawan da suka taru don yaƙi. Mutanen Isra'ila kuwa suka jā baya,

10. shi kuwa ya tsaya, ya yi ta yaƙi da Filistiyawa, har hannunsa ya ƙage, har bai iya ɓanɓaruwa daga takobinsa ba. Ubangiji ya ba da babbar nasara a wannan rana. Bayan an gama sai Isra'ilawa suka koma wurin Ele'azara don su kwashi ganima kawai.

11. Biye da Ele'azara kuma, sai Shamma, ɗan Agi, daga Harod. Filistiyawa suka taru a Lihai, inda akwai wata gonar wake. Isra'ilawa kuwa suka guji wa Filistiyawa.

12. Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta. Ya kuma kashe Filistiyawa. Ubangiji ya ba da babbar nasara.

13. Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.

14. Dawuda yana cikin kagara, ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuwa tana a Baitalami.

15. Dawuda ya ji marmari, ya ce, “Kai, da ma wani zai ba ni ruwan rijiyar ƙofar garin Baitalami in sha!”

16. Shahararrun jarumawan nan uku kuwa suka sheƙa a guje, suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka tafi, suka ɗebo ruwa daga rijiyar ƙofar garin Baitalami, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda bai sha ba, ya zuba shi hadaya a gaban Ubangiji.

17. Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji, ka tsare ni daga shan jinin mutanen da suka sadaukar da ransu.” Saboda haka bai sha ruwan ba.Abubuwan da jarumawan nan uku suka yi ke nan.

18. Abishai, ɗan'uwan Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban jarumawan nan talatin. Sa'ad da ya girgiza mashinsa, sai da ya kashe mutum ɗari uku. Da haka ya samar wa kansa sūna tare da mutanen nan uku.

19. Shi ya fi shahara daga cikin su talatin ɗin, don haka ya zama shugabansu, amma bai kai su uku ɗin can ba.

20. Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo.

21. Ya kuma kashe wani Bamasare mai cika fuska. Bamasaren yana da māshi a hannunsa, amma Benaiya ya tafi wurinsa da sanda, ya fizge mashin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da māshin.

22. Abubuwan da Benaiya, ɗan Yehoyada ya yi ke nan. Da haka ya samar wa kansa suna tare da jarumawan nan talatin.

23. Ya shahara cikin jarumawan nan talatin, amma bai kai su uku ɗin can ba. Dawuda kuwa ya maishe shi ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

24-39. Sauran jarumawan da suka zama talatin sun haɗu da waɗannan,Asahel, ɗan'uwan Yowab,Elhanan, ɗan Dodo, daga Baitalami,Shamma da Elika, daga Harod,Helez, daga Felet,Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa,Abiyezer, daga Anatot,Sibbekai, daga Husha,Zalmon, daga Aho,Maharai, da Heled, ɗan Ba'ana, daga Netofa,Ittayi, ɗan Ribai, daga Gibeya ta Biliyaminu,Benaiya, daga Firaton,Hurai, daga kwaruruka kusa da Ga'ash,Abiyel, daga Araba,Azmawet, daga Bahurim,Eliyaba, daga Shalim,Yashen, daga Gimzo,Jonatan, ɗan Shamma, daga Harod,Ahiyam, ɗan Sharar, daga Harod,Elifelet, ɗan Ahasbai, daga Ma'aka,Eliyam, ɗan Ahitofel, daga Gilo,Hezro, daga Karmel,Nayarai, daga Arabiya,Igal, ɗan Natan, daga Zoba,Bani, daga Gad,Zelek, daga Ammon,Naharai, (mai ɗaukar wa Yowab, ɗan Zeruya makamai) daga Biyerot,Aira daga Gareb, daga Yattir,Uriya, Bahitte.Dukansu su talatin da bakwai ne shahararrun sojoji.

Karanta cikakken babi 2 Sam 23