Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 16:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Da jin haka sai sarki ya ce wa Ziba, “Dukan abin da yake na Mefiboshet ya zama naka.”Ziba kuma ya rusuna ya yi godiya ya ce, “Bari in zama majidaɗin ubangijina, sarki.”

5. Sa'ad da Dawuda ya kai Bahurim, sai ga wani mutum sunansa Shimai, ɗan Gera, daga iyalin gidan Saul, ya fito yana ta zagi.

6. Ya jajjefi Dawuda da fādawansa da duwatsu, da sauran jama'a, da dukan jarumawan da suke kewaye da shi.

7. Shimai ya yi ta zagi, yana cewa, “Tafi, tafi, kai mai kisankai, sakarai.

8. Ubangiji ya sāka maka saboda alhakin jinin gidan Saul, wanda ka hau gadon sarautarsa. Yanzu Ubangiji ya ba da sarautar ga Absalom, ɗanka. Duba, masifa ta auko maka, gama kai mai kisankai ne.”

9. Sai Abishai, ɗan Zeruya, ya ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, don me za ka bar wannan kare yana ta zaginka? Bari in tafi in fille masa kai.”

10. Amma sarki ya ce masa, “Ba ruwanku, ku 'ya'yan Zeruya. Idan yana zagi saboda Ubangiji ya sa shi, to, wa ya isa ya ce, ‘Don me kake yin haka?’ ”

11. Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.

12. Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.”

13. Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature.

Karanta cikakken babi 2 Sam 16