Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 15:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'ad da mutum ya je kusa da shi ya rusuna don ya gaishe shi, Absalom kuwa yakan rungume mutumin ya sumbace shi.

6. Haka Absalom ya riƙa yi wa dukan Isra'ilawan da suka zo wurin sarki don shari'a. Da haka ya saci zukatan mutanen Isra'ila.

7. Bayan shekara huɗu sai Absalom ya ce wa sarki, “Ina roƙonka, ka yardar mini in je Hebron in cika wa'adina wanda na yi wa Ubangiji.

8. Gama na yi wa'adi sa'ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa'adi cewa, ‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.’ ”

9. Sarki ya ce masa, “To, ka sauka lafiya.” Sai ya tashi ya tafi Hebron.

10. Amma Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra'ila a faɗa musu haka, “Da zarar kun ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom shi ne sarki, yana Hebron.’ ”

11. Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.

12. Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.

13. Ana nan sai wani manzo ya zo wurin Dawuda, ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra'ila suna wajen Absalom.”

14. Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”

15. Fādawan suka ce, “Mu a shirye muke mu yi dukan abin da ubangijinmu sarki ya faɗa.”

16. Sarki ya fita, iyalinsa suka bi shi, amma ya bar ƙwaraƙwarai goma su lura da gidan.

17. Sarki ya fita yana tafiya da ƙafa, dukan mutane kuwa suna biye da shi. Da suka zo Bet-Merhak, wato gida na ƙarshe sai suka tsaya.

Karanta cikakken babi 2 Sam 15