Haka Absalom ya riƙa yi wa dukan Isra'ilawan da suka zo wurin sarki don shari'a. Da haka ya saci zukatan mutanen Isra'ila.