Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 12:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Amma talakan ba shi da kome sai 'yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da 'ya'yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar 'ya a gare shi.

4. Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo 'yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”

5. Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa.

6. Sai kuma ya biya diyyar 'yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”

7. Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra'ila, na cece ka daga hannun Saul.

8. Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra'ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.

9. Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.

10. Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.

11. Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā.

12. Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra'ila da rana katā.’ ”

13. Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.

14. Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”

15. Sa'an nan Natan ya tafi gida.Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.

16. Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.

Karanta cikakken babi 2 Sam 12