Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 9:4-6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4-6. Iyalin Yahuza guda ɗari shida da tasa'in suka zauna a Urushalima, shugabansu kuwa shi ne Utai ɗan Ammihud, jīkan Omri daga wajen Feresa. Waɗansu kakanninsu kuwa su ne Imri da Bani. Zuriyar Shela ɗan Yahuza suna da shugaba mai suna Asaya. Zuriyar Zera ɗan Yahuza kuwa, shugabansu Yuwel.

7. Ga zuriyar Biliyaminu a Urushalima bi da bi, da Sallai ɗan Meshullam, da Hodawiya, da Hassenuwa,

8. da kuma Ibneya ɗan Yeroham, da Ila ɗan Uzzi, wato jīkan Mikri, da Meshullam ɗan Shefatiya, da Reyuwel, da Ibnija.

9. Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.

10. Daga cikin firistoci masu zama a Urushalima su ne Yedaiya, da Yehoyarib, da Yakin,

11. da Azariya ɗan Hilkiya, shi ne jami'in Haikalin Ubangiji, kakanninsa sun haɗu da Shallum ɗan Zadok, da Merayot, da Ahitub,

12. da Adaya ɗan Yeroham, kakanninsa sun haɗu da Fashur, da Malkiya, da Ma'asai ɗan Adiyel, kakanninsa sun haɗu da Yazera, da Meshullam, da Meshillemot, da Immer.

13. Firistacin da suke shugabannin gidajen kakanninsu, sun kai mutum dubu da ɗari bakwai da sittin (1,760). Ƙwararru ne cikin hidimar Haikalin Ubangiji.

14. Lawiyawa masu zama a Urushalima kuma, su ne Shemaiya ɗan Hasshub, wanda kakanninsa suka haɗu da Azrikam da Hashabiya daga 'ya'yan Merari, maza,

15. da kuma Bakbakkar, da Heresh, da Galal, da Mattaniya ɗan Mika wanda kakanninsa su ne Zikri da Asaf,

16. da kuma Obadiya ɗan Shemaiya, kakanninsa su ne Galal da Yedutun, da Berikiya ɗan Asa, wato jīkan Elkana, wanda ya zauna a garin Netofa.

17. Masu tsaron Haikalin, su ne Shallum, da Akkub, da Talmon, da Ahiman, da 'yan'uwansu. Shallum shi ne shugaba.

18. Har zuwa yau, iyalinsu suke tsaron ƙofar sarki a wajen gabas. A dā su ne suke tsaron sauran ƙofofin zangon Lawiyawa.

19. Shallum ɗan Kore, wato jīkan Ebiyasaf, tare da 'yan'uwansa na zuriyar Kora, suke lura da masu tsaron ƙofofin alfarwa kamar dai yadda kakanninsu suka lura da zangon Ubangiji.

20. A dā Finehas ɗan Ele'azara shi ne shugabansu, Ubangiji kuwa yana tare da shi.

21. Zakariya ɗan Shallum yake tsaron ƙofar alfarwa ta sujada.

Karanta cikakken babi 1 Tar 9