Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 9:10-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa.

11. Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al'ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.

12. Amma sa'ad da Hiram ya zo daga Taya domin ya ga garuruwan da Sulemanu ya ba shi, sai ya ga ba su gamshe shi ba.

13. Don haka ya ce wa Sulemanu, “Dan'uwa, waɗanne irin garuruwa ke nan da ka ba ni?” Saboda haka har yanzu ana kiran ƙasar Kabul, wato marar amfani.

14. Hiram kuma ya aika wa Sulemanu da zinariya mai nauyin talanti ɗari da ashirin.

15. Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer.

16. Gama Fir'auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa'an nan ya yi wa 'yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin.

17. Sulemanu kuwa ya sāke gina Gezer. Ya kuma sa aka gina Bet-horon ta kwari ta aikin tilas,

18. da Ba'alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza,

19. da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.

20-21. Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, da suka ragu a ƙasar, wato waɗanda ba mutanen Isra'ila ba, waɗanda mutanen Isra'ila ba su iya hallakarwa ba, Sulemanu ya sa zuriyarsu su yi aikin tilas na bauta, haka kuwa suke har wa yau.

22. Sulemanu bai mai da mutanen Isra'ila bayi ba, amma su ne sojojinsa da dogaransa, da shugabannin sojoji, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.

23. Sulemanu yana da masu lura da aiki su ɗari biyar da hamsin, suna lura da masu aikin tilas a wurare dabam dabam da ake wa Sulemanu gini.

24. Da 'yar Fir'auna matar Sulemanu ta fita birnin Dawuda, zuwa gidan kanta wanda Sulemanu ya gina mata, sa'an nan ya gina birnin Millo.

25. Sau uku a shekara Sulemanu yakan miƙa hadayu na ƙonawa, da na salama, da hadayar turare, a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji. Ta haka aka gama ginin Haikali.

26. Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom.

27. Sarki Hiram ya aiki barorinsa, gogaggun matuƙan jiragen ruwa, da jiragen ruwa tare da barorin Sulemanu.

Karanta cikakken babi 1 Sar 9