Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 5:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'an nan Hiram ya aika wurin Sulemanu, ya ce, “Na ji saƙonka da ka aiko mini, a shirye nake in yi maka dukan abin da kake bukata a kan katakan itacen al'ul, da na fir.

9. Barorina za su kawo su daga Lebanon zuwa teku. Zan sa a yi gadon fito da su, su bi teku zuwa inda kake so, a can mutanena za su warware su, sa'an nan naka mutane su kwashe su. Kai kuma ka ba da abinci ga mutanena.”

10. Sai Hiram ya ba Sulemanu dukan katakan itacen al'ul da na fir da yake bukata,

11. Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma'auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.

12. Ubangiji kuwa ya ba Sulemanu hikima kamar yadda ya yi masa alkawari. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Hiram da Sulemanu, suka kuma ƙulla yarjejeniya da juna.

13. Sarki Sulemanu kuwa ya sa a yi aikin tilas daga cikin Isra'ila duka. Waɗanda aka samu da za su yi aikin tilas ɗin mutum dubu talatin (30,000) ne.

14. Ya riƙa aikawa da su zuwa Lebanon, ya raba su mutum dubu goma goma (10,000) su yi wata ɗaya ɗaya, sa'an nan su komo gida su yi wata biyu biyu. Adoniram shi ne shugaban aikin tilas ɗin.

15. Sulemanu kuma yana da mutum dubu saba'in (70,000) a ƙasar tuddai masu haƙar duwatsu, da dubu tamanin (80,000) masu ɗauko duwatsun.

16. Banda waɗannan kuma, Sulemanu ya sa shugabanni dubu uku da ɗari uku (3,300) waɗanda suke lura da aikin, da mutanen da suke yin aikin.

17. Bisa ga umarnin sarki Sulemanu suka sassaƙa manyan duwatsu kyawawa don kafa harsashin ginin Haikali.

18. Sai maginan Sulemanu, da na Hiram, da mutanen Gebal suka shirya duwatsu da katakai da za a gina Haikalin.

Karanta cikakken babi 1 Sar 5