Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 20:20-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.

21. Sarkin Isra'ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.

22. Sa'an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra'ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”

23. Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka.

24. Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu.

25. Sa'an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.”Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi haka nan.

26. Da shekara ta juyo, sai Ben-hadad ya tara Suriyawa, suka haura zuwa Afek don su yi yaƙi da Isra'ilawa.

27. Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.

28. Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama'a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”

29. Suka kafa sansani daura da juna kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin, suka kama yaƙi. Isra'ilawa suka kashe Suriyawa mutum dubu ɗari (100,000) a rana ɗaya.

30. Sauran kuwa suka gudu zuwa birnin Afek. Garun birnin kuma ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai (27,000) waɗanda suka ragu.Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga ƙurewar ɗaki, a cikin birnin.

31. Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra'ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa'an nan mu tafi wurin Sarkin Isra'ila, watakila zai bar ka da rai.”

32. Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra'ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.”Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan'uwana ne.”

33. Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan'uwanka, Ben-hadad.”Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.

34. Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.”Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.

Karanta cikakken babi 1 Sar 20