Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:30-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.”Amma Yowab ya ce, “A'a, a nan zan mutu.”Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.

31. Sarki kuwa ya ce masa, “Ka yi yadda ya ce, ka kashe shi, ka binne shi, ta haka za ka kawar mana da hakkin jinin da Yowab ya zubar ba dalili.

32. Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.

33. Don haka alhakin jininsu zai koma a kan zuriyar Yowab har abada, amma da Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da gadon sarautarsa, albarkar Ubangiji za ta zauna a kansu har abada.”

34. Benaiya ɗan Yehoyada kuwa ya shiga alfarwar ya kashe shi. Aka binne shi a gidansa a karkara.

35. Sa'an nan sarki ya naɗa Benaiya ɗan Yehoyada, shugaban sojoji a maimakon Yowab, ya kuma naɗa Zadok, firist, a maimakon Abiyata.

36. Sai kuma sarki ya aika a kirawo Shimai. Sa'an nan ya ce masa, “Ka gina wa kanka gida a Urushalima, ka zauna a nan, kada ka fita ko kaɗan zuwa wani wuri.

37. Gama ran da ka fita, ka haye rafin Kidron, ka tabbata fa za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”

38. Shimai kuwa ya ce wa sarki, “Abin da ka faɗa daidai ne, abin da ka ce in yi, zan yi, ranka ya daɗe.” Sai Shimai ya zauna a Urushalima kwanaki da yawa.

39. Amma bayan shekara uku, sai biyu daga cikin bayin Shimai suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma'aka, Sarkin Gat. Da aka faɗa wa Shimai, cewa bayinsa suna a Gat,

40. sai ya tashi, ya yi wa jakinsa shimfiɗa, ya tafi Gat wurin Akish don neman bayinsa. Ya kuwa komo da bayinsa daga Gat.

Karanta cikakken babi 1 Sar 2