Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:26-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.”

27. Saboda haka Sulemanu ya kori Abiyata daga aikin firist na Ubangiji, ta haka aka cika maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Eli a Shilo.

28. Da Yowab ya ji labari, gama har shi ya goyi bayan Adonija, ko da yake bai goyi bayan Absalom ba, sai ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ya kama zankayen bagade.

29. Sa'ad da aka faɗa wa sarki Sulemanu, Yowab ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ga shi, yana wajen bagade, sai Sulemanu ya aiki Benaiya, ɗan Yehoyada, ya je ya kashe shi.

30. Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.”Amma Yowab ya ce, “A'a, a nan zan mutu.”Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.

31. Sarki kuwa ya ce masa, “Ka yi yadda ya ce, ka kashe shi, ka binne shi, ta haka za ka kawar mana da hakkin jinin da Yowab ya zubar ba dalili.

32. Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.

Karanta cikakken babi 1 Sar 2