Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 17:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”

5. Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa, ya tafi ya zauna a rafin Kerit wanda yake gabashin Urdun.

6. Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin.

7. Da aka jima sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar.

8. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya.

9. “Tashi ka tafi Zarefat ta Sidon, ka zauna a can. Ga shi, na umarci wata mace wadda mijinta ya rasu ta ciyar da kai.”

10. Sai ya tashi, ya tafi Zarefat. Sa'ad da ya isa ƙofar garin, sai ga wata wadda mijinta ya rasu tana tattara itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa in sha.”

11. Ta juya ta tafi don ta kawo masa ruwan sha ke nan, sai ya sāke kiranta, ya ce, “Ki kuma kawo mini ɗan abinci.”

12. Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”

13. Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini 'yar waina, ki kawo mini, sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki.

14. Gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Garin da yake a tukunyarki ba zai ƙare ba, man da yake a kurtunki kuma ba zai ƙare ba, sai ran da Ubangiji ya sa aka yi ruwan sama a ƙasar.’ ”

Karanta cikakken babi 1 Sar 17