Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 13:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai ga annabi ya fito daga Yahuza zuwa Betel. Yerobowam kuwa yana tsaye kusa da bagaden don ya ƙona turare.

2. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai annabin ya ta da murya, ya ce, “Ya bagade, bagade, Ubangiji ya ce za a haifi ɗa a gidan Dawuda, sunansa Yosiya wanda zai miƙa firistoci na masujadan tuddai hadaya a kanka, wato firistoci waɗanda suke ƙona turare. Za a ƙone ƙasusuwan mutane a bisa kanka.”

3. Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”

4. Da sarki ya ji maganar annabin, wato wadda ya yi a kan bagaden da yake Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden, ya ce, “Ku kama shi.” Hannun da ya miƙa kuwa ya sage, bai iya komo da shi ba.

5. Aka rushe bagaden, aka kuma zubar da tokar daga bagaden bisa ga alamar da annabin ya faɗa da sunan Ubangiji.

6. Sarki Yerobowam ya ce wa annabin, “In ka yarda ka yi roƙo ga Ubangiji Allahnka domina, ka yi mini addu'a don ya warkar da hannuna.”Annabi ya roƙi Ubangiji, sai hannun sarki ya komo daidai.

7. Sa'an nan sarkin ya ce wa annabin, “Zo mu tafi gida don ka shaƙata, zan ba ka lada.”

8. Annabin kuwa ya ce wa sarki, “Ko da za ka ba ni rabin gidanka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuma zan ci abinci ko in sha ruwa a wurin nan ba.

9. Gama Ubangiji ya umarce ni da cewa kada in ci abinci, ko in sha ruwa, ko in koma ta hanyar da na zo.”

10. Haka kuwa ya koma ta wata hanya dabam bai koma ta hanyar da ya bi zuwa Betel ba.

11. Akwai wani tsohon annabi a Betel. 'Ya'yansa maza kuwa suka tafi suka faɗa masa dukan abin da annabin Allah ya yi a Betel a wannan rana. Suka faɗa wa mahaifinsu maganar da annabin Allah ya faɗa wa sarki.

12. Tsohon annabin ya tambaye su, “Wace hanya ya bi?” Su kuwa suka nuna masa hanyar.

13. Ya ce musu su ɗaura wa jakinsa shimfiɗa. Sai suka ɗaura wa jakin shimfiɗa, shi kuwa ya hau,

14. ya bi bayan annabin nan da ya fito daga Yahuza, ya same shi yana zaune a gindin itace oak. Ya tambaye shi, “Ko kai ne annabin da ya zo daga Yahuza?”Mutumin ya amsa, “I, ni ne,”

Karanta cikakken babi 1 Sar 13