Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 9:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Saul ya ce wa baransa, “Idan muka tafi, me za mu ba shi? Gama guzurin da yake tare da mu ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu ba shi.”

8. Baran kuma ya ce wa Saul, “Ina da 'yar azurfa tsaba da zan ba shi domin ya faɗa mana inda za mu same su.”

9. (A dā a Isra'ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.)

10. Sai Saul ya ce wa baransa, “Maganarka daidai ce, zo, mu tafi.” Suka kuwa tafi garin da mutumin Allah yake.

11. Sa'ad da suka haura zuwa garin, suka gamu da waɗansu 'yan mata za su ɗebo ruwa, suka ce musu, “Maigani yana nan?”

12. 'Yan matan suka amsa, suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi nan ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu.

13. Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”

14. Suka kuwa haura zuwa cikin garin. Da shigarsu suka ga Sama'ila ya nufo wajen da suke, za shi wurin da ake yin sujadar.

15. Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama'ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama'ila.

16. Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama'ata Isra'ila. Zai ceci jama'ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama'ata suke sha, gama na ji kukansu.”

17. Da Sama'ila ya ga Saul, sai Ubangiji ya ce masa, “To, ga mutumin da na faɗa maka! Shi ne wanda zai sarauci jama'ata.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 9