Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 4:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wannan lokaci Isra'ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra'ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek.

2. Filistiyawa suka shirya su fara yaƙi. Bayan yaƙi mai zafi, sai Filistiyawa suka ci Isra'ilawa, suka kashe mutane wajen dubu huɗu (4,000) a bakin dāga.

3. Da sojojin da suka ragu suka koma sansani, sai shugabannin Isra'ila suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa Filistiyawa suka ci mu yau? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo ya kasance tare da mu, ya cece mu daga ikon abokan gābanmu.”

4. Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. 'Ya'yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin.

5. Da akwatin alkawarin Ubangiji ya iso sansanin, sai dukan mutanen Isra'ila suka yi sowa da ƙarfi, har ƙasa ta amsa.

6. Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma'anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin,

7. sai Filistiyawa suka tsorata, suka ce, “Allah ya shiga sansanin, kaitonmu, gama ba a taɓa yin irin wannan abu ba.

8. Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada!

9. Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 4