Filistiyawa suka shirya su fara yaƙi. Bayan yaƙi mai zafi, sai Filistiyawa suka ci Isra'ilawa, suka kashe mutane wajen dubu huɗu (4,000) a bakin dāga.