Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Filistiyawa Sun Ƙwace Akwatin Alkawari

1. A wannan lokaci Isra'ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra'ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek.

2. Filistiyawa suka shirya su fara yaƙi. Bayan yaƙi mai zafi, sai Filistiyawa suka ci Isra'ilawa, suka kashe mutane wajen dubu huɗu (4,000) a bakin dāga.

3. Da sojojin da suka ragu suka koma sansani, sai shugabannin Isra'ila suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa Filistiyawa suka ci mu yau? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo ya kasance tare da mu, ya cece mu daga ikon abokan gābanmu.”

4. Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. 'Ya'yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin.

5. Da akwatin alkawarin Ubangiji ya iso sansanin, sai dukan mutanen Isra'ila suka yi sowa da ƙarfi, har ƙasa ta amsa.

6. Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma'anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin,

7. sai Filistiyawa suka tsorata, suka ce, “Allah ya shiga sansanin, kaitonmu, gama ba a taɓa yin irin wannan abu ba.

8. Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada!

9. Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”

10. Filistiyawa kuwa suka yi yaƙi gadan-gadan, suka ci mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka gudu, kowa ya nufi gidansa. Aka kashe Isra'ilawa da yawa, wato mutum dubu talatin (30,000).

11. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji, 'ya'yan Eli guda biyu, Hofni da Finehas kuma, aka kashe su.

Mutuwar Eli

12. Wani mutumin kabilar Biliyaminu ya gudu daga dāgar yaƙin ya zo Shilo da tufafinsa ketattu ga kuma ƙura a kansa.

13. Sa'ad da ya iso, Eli yana zaune a kujerarsa a bakin hanya, yana jira, gama zuciyarsa ta damu saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shiga gari ya ba da labari, dukan garin ya ruɗe da kuka.

14. Sa'ad da Eli ya ji kukan, sai ya tambaya ya ce, “Me ake wa kuka?” Mutumin kuwa ya gaggauta zuwa wurin Eli ya faɗa masa.

15. (Eli yana da shekara tasa'in da takwas, ya kuwa makance ɗungum.)

16. Mutumin ya ce wa Eli, “Yau daga wurin yaƙin na tsere, na gudo gida.”Eli ya ce, “Dana, me ya faru?”

17. Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra'ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

18. Da aka ambaci akwatin alkawari, sai Eli ya tuntsura da baya daga inda yake zaune a bakin ƙofar gari, wuyansa kuwa ya karye, ya mutu, gama shi tsoho ne, mai ƙiba. Ya shekara arba'in yana shugabancin Isra'ila.

Mutuwar Matar Finehas

19. Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa'ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu.

20. Tana bakin mutuwa, matan kuwa da take taimakonta suka ce mata, “Ki yi ƙarfin hali, gama kin haifi ɗa namiji.” Amma ba ta amsa ba, ba ta kuma kula ba.

21. Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra'ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu.

22. Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra'ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”