Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 23:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Aka faɗa wa Dawuda, cewa Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Kaila, suna washe musu hatsi a masussukai.

2. Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?”Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”

3. Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, nan ma a Yahuza muna jin tsoro, balle mu tafi Kaila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa.”

4. Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”

5. Sa'an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Kaila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kashe su da yawa, suka kwashe shanunsu. Da haka Dawuda ya kuɓutar da mazaunan Kaila.

6. Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek, ya gudu zuwa wurin Dawuda a Kaila, ya zo da falmaran a hannunsa.

7. Aka faɗa wa Saul Dawuda ya zo Kaila. Sai ya ce, “Madalla, Allah ya bashe shi a hannuna, gama ya kulle kansa, da yake ya shiga garin da yake da ƙofofin da akan kulle da sandunan ƙarfe.”

8. Saul ya kirawo dukan mutanensa, su fita yaƙi, su tafi Kaila don su kewaye Dawuda tare da mutanensa.

9. Dawuda kuwa ya sani Saul yana shirya hanyar kashe shi, sai ya ce wa Abiyata, firist, “Kawo falmaran a nan.”

10. Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, hakika bawanka ya ji Saul yana niyyar zuwa Kaila don ya hallakar da garin saboda ni.

11. Ko mutanen Kaila za su bashe ni a hannunsa? Ko Saul zai zo kamar yadda na ji? Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ina roƙonka ka faɗa wa bawanka.”Ubangiji kuwa ya ce, “Saul zai zo.”

12. Dawuda kuma ya ce, “Mutanen Kaila za su bashe ni da mutanena a hannun Saul?”Ubangiji ya ce masa, “Za su bashe ku.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 23