Sa'an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Kaila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kashe su da yawa, suka kwashe shanunsu. Da haka Dawuda ya kuɓutar da mazaunan Kaila.