Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 2:9-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Zai kiyaye rayukan amintattunmutanensa,Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu,Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.

10. Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji,Zai yi musu tsawa daga Sama.Ubangiji zai hukunta dukan duniya,Zai ba sarkinsa iko,Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zamamai nasara.”

11. Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.

12. 'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba,

13. Ko ka'idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama'a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa'ad da ake dafa naman.

14. Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra'ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo.

15. Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.”

16. Idan mutumin ya ce, “To, bari a ƙona kitsen tukuna, sa'an nan ka ɗibi iyakar abin da kake bukata,” sai baran firist ɗin ya ce, “A'a, tilas ne ka ba ni yanzu, idan kuwa ba haka ba, zan ɗiba ƙarfi da yaji!”

17. Zunubin 'ya'yan nan maza na Eli ya yi yawa a gaban Ubangiji, gama sun wulakanta hadayar Ubangiji ƙwarai da gaske.

18. Yaron nan Sama'ila yana ta aiki gaban Ubangiji, yana sāye da falmaran.

19. A kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka 'yar rigar ado, ta kai masa a sa'ad da ita da mijinta sukan tafi miƙa hadayarsu ta shekara shekara.

20. Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu 'ya'ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.”Bayan wannan sai su koma gida.

21. Ubangiji ya sa wa Hannatu albarka, ta haifi 'ya'ya maza uku da mata biyu. Yaron nan Sama'ila kuwa ya girma a gaban Ubangiji.

22. Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da 'ya'yansa maza suke yi wa Isra'ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

23. Sai ya ce musu, “Me ya sa kuke irin waɗannan abubuwa? Gama kowa yana faɗa mini irin mugayen abubuwan da kuke aikatawa.

24. Haba 'ya'yana, ku bari! Jama'ar Ubangiji suna ta magana a kan wannan mugun abu.

25. Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?”Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.

26. Yaron nan Sama'ila ya yi ta girma da samun tagomashi a gaban Ubangiji da kuma mutane.

Karanta cikakken babi 1 Sam 2