Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 2:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce,“Ubangiji ya cika zuciyata da murna.Ina farin ciki da abin da ya yi.Ina yi wa maƙiyana dariya,Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.

2. “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji,Babu wani mai kama da shi,Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.

3. Kada ku ƙara yin magana ta girmankai,Ku daina maganganunku na fariya,Gama Ubangiji Allah shi ne masani,Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.

4. An kakkarya bakunan ƙarfafan sojoji,Amma rarrauna ya zama mai ƙarfi.

5. Ƙosassun mutane suna ƙodago saboda abinci,Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa.Bakarariya ta haifi 'ya'ya bakwai,Wadda ta haifi 'ya'ya da yawa kuwata rasa su duka.

6. Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar,Yana kai mutane kabari,Ya kuma tā da su.

7. Yakan sa waɗansu mutane su zamamatalauta,Waɗansu kuwa attajirai.Yakan ƙasƙantar da waɗansu,Ya kuma ɗaukaka waɗansu.

8. Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura,Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki.Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki,Ya ɗora su a wurare masu maƙami.Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne,A kansu ya kafa duniya.

9. “Zai kiyaye rayukan amintattunmutanensa,Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu,Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.

10. Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji,Zai yi musu tsawa daga Sama.Ubangiji zai hukunta dukan duniya,Zai ba sarkinsa iko,Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zamamai nasara.”

11. Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.

12. 'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba,

13. Ko ka'idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama'a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa'ad da ake dafa naman.

14. Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra'ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo.

15. Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.”

16. Idan mutumin ya ce, “To, bari a ƙona kitsen tukuna, sa'an nan ka ɗibi iyakar abin da kake bukata,” sai baran firist ɗin ya ce, “A'a, tilas ne ka ba ni yanzu, idan kuwa ba haka ba, zan ɗiba ƙarfi da yaji!”

Karanta cikakken babi 1 Sam 2