Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 18:19-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Amma sa'ad da lokaci ya yi da za a ba Dawuda Merab, 'yar Saul, ya aura, sai aka aurar da ita ga Adriyel, mutumin Abel-mehola.

20. Mikal, 'yar Saul kuwa, ta ƙaunaci Dawuda, sai aka faɗa wa Saul, shi kuwa ya yarda da haka.

21. Ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan ba shi ita don ta zamar masa sanadin da zai mutu ta hannun Filistiyawa.” Don haka sai Saul ya ce wa Dawuda a karo na biyu, “Yanzu dai za ka zama surukina.”

22. Sai Saul ya umarci fādawansa, ya ce, “Ku yi magana da Dawuda a ɓoye, ku ce masa, ‘Ga shi, sarki yana jin daɗinka, dukan fādawansa kuma suna ƙaunarka, yanzu sai ka zama surukin sarki.’ ”

23. Fādawan Saul kuwa suka faɗa wa Dawuda wannan magana. Sai Dawuda ya ce, “Zama surukin sarki ƙaramin abu ne a ganinku? Ga shi, ni talaka ne wanda ba sananne ba.”

24. Fādawan suka faɗa wa Saul abin da Dawuda ya faɗa.

25. Saul kuma ya ce, “Haka za ku faɗa wa Dawuda, ‘Sarki ba ya so ka ba da sadaki don auren, sai dai ka ba da loɓar Filistiyawa guda ɗari, domin ka ɗauki fansa a kan maƙiyan sarki.’ ” (Saul dai yana so Filistiyawa su kashe Dawuda kawai.)

26-27. Da fādawan suka faɗa wa Dawuda abin da Saul ya ce, sai Dawuda ya ji daɗi ƙwarai ya zama surukin sarki. Kafin lokacin da aka yanka masa ya yi, sai Dawuda ya tashi, ya tafi tare da mutanensa, suka kashe Filistiyawa ɗari biyu. Ya kawo loɓarsu duka, aka ba sarki, domin ya zama surukin sarki. Saul kuwa ya aurar da Mikal, 'yarsa, ga Dawuda.

28-29. Da Saul ya gane lalle Ubangiji yana tare da Dawuda, Mikal 'yarsa kuma tana ƙaunar Dawuda, sai ya ƙara jin tsoronsa, ya maishe shi maƙiyinsa na din din din.

30. Sarakunan Filistiyawa sukan zo da yaƙi. Idan sun zo, sai Dawuda ya yi nasara da su fiye da sauran shugabannin yaƙi na Saul. Wannan ya sa ya yi suna.

Karanta cikakken babi 1 Sam 18