Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 19:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. An yardar mata ta sa tufafin lallausan lilinmai ɗaukar ido, mai tsabta.”Lallausan lilin ɗin nan, shi ne aikin adalci na tsarkaka.

9. Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”

10. Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.

11. Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.

12. Idanunsa kamar harshen wuta suke, kansa da kambi da yawa, yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi.

13. Yana saye da riga wadda aka tsoma a jini, sunan da ake kiransa da shi kuma, shi ne Kalman Allah.

14. Rundunonin Sama, saye da lallausan lilin fari mai tsabta, suna a biye da shi a kan fararen dawakai.

15. Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi yake fitowa, wanda zai sare al'ummai da shi, zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi, ta tsananin fushin Allah Maɗaukaki.

16. Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.

Karanta cikakken babi W. Yah 19