Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 14:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,

5. ba wata ƙarya a bakinsu, domin su marasa aibu ne.

6. Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.

7. Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi. Ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa.”

8. Sai kuma mala'ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ita da ta zuga dukkan al'ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”

9. Sai kuma mala'ika na uku ya biyo, yana ɗaga murya da ƙarfi, yana cewa, “Duk mai yi wa dabbar nan da siffarta sujada, wanda kuma ya yarda a yi masa alama a goshinsa, ko a hannunsa,

10. zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala'iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.

11. Hayaƙin azabar nan tasu ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato, waɗannan masu yi wa dabbar nan da siffarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”

12. Wannan yana nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.

13. Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”

Karanta cikakken babi W. Yah 14