Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 14:14-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.

15. Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”

16. Yesu ya ce, “Ba lalle su tafi ba. Ku ku ba su abinci mana.”

17. Sai suka ce masa, “Ai, gurasa biyar da kifi biyu kawai muke da su a nan.”

18. Sai ya ce, “Ku kawo mini su.”

19. Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.

20. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu.

21. Waɗanda suka ci kuwa misalin maza dubu biyar ne banda mata da yara.

22. Sai ya sa almajiransa suka shiga jirgi su riga shi hayewa kafin ya sallami taron.

23. Bayan ya sallami taron, ya hau dutse shi kaɗai domin ya yi addu'a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai.

24. Sa'an nan kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa mangara tasa, gama iska tana gāba da su.

25. Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.

26. Sa'ad da kuwa almajiran suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka firgita suka ce, “Fatalwa ce!” Suka yi kururuwa don tsoro.

27. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, Ni ne, kada ku ji tsoro.”

28. Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka a kan ruwan.”

29. Ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya nufi gun Yesu.

30. Amma da ya ga iska ta yi ƙarfi sai ya ji tsoro. Da ya fara nutsewa sai ya yi kururuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”

31. Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

32. Da shigarsu jirgin iska ta kwanta.

Karanta cikakken babi Mat 14