Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 8:20-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.”

21. Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma 'yan'uwana.”

22. Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi.

23. Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Hadiri mai iska ya taso a tekun, jirginsu ya tasar wa cika da ruwa, har suna cikin hatsari.

24. Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.

25. Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

26. Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda take hannun riga da ƙasar Galili.

27. Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta.

28. Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”

29. Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji.

30. Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.

31. Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahalaka.

Karanta cikakken babi Luk 8