Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 8:14-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.

15. Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.

16. “Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

17. Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba.

18. Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”

19. Uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro.

20. Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.”

21. Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma 'yan'uwana.”

22. Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi.

Karanta cikakken babi Luk 8