Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 6:39-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba?

40. Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa.

41. Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

42. Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, ‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”

43. “Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan 'ya'ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan 'ya'ya.

44. Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.

45. Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”

46. “Don me kuke kirana, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku?

47. Duk mai zuwa wurina, yake jin maganata, yake kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa.

48. Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci.

49. Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”

Karanta cikakken babi Luk 6