Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 6:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci.

2. Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Don me kuke yin abin da bai halatta a yi ba a ran Asabar?”

3. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?

4. Yadda ya shiga masujadar Allah, ya ɗauki keɓaɓɓiyar gurasan nan ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa, wadda ba ta halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai?”

5. Sai ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”

6. A wata Asabar kuma ya shiga majami'a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye.

7. Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.

8. Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin.

9. Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?”

10. Sai ya duddube su duke, ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa, hannunsa kuwa sai ya koma lafiyayye.

11. Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.

12. A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah.

Karanta cikakken babi Luk 6