Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 24:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa.

11. Su kuwa sai maganan nan ta zama musu kamar zance ne kawai, suka ƙi gaskatawa.

12. Amma Bitrus ya tashi, ya doshi kabarin da gudu. Ya duƙa, ya leƙa a ciki, ya ga likkafanin lilin a ajiye waje ɗaya. Sai ya koma gida yana al'ajabin abin da ya auku.

13. A ran nan kuma sai ga waɗansu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imuwasu, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne.

14. Suna ta zance da juna a kan dukan al'amuran da suka faru.

15. Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare.

16. Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba.

17. Yesu ya ce musu, “Wace magana ce kuke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna baƙin ciki.

18. Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, 'yan kwanakin nan ba?”

19. Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “Game da Yesu Banazare ne, wanda yake annabi mai manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana a gaban Allah da dukan mutane,

20. da kuma yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa gicciye shi.

21. Dā kuwa muna bege shi ne zai fanshi Isra'ila. Hakika kuma, bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abu.

22. Har wa yau kuma, waɗansu mata na cikinmu, sun ba mu al'ajabi. Don sun je kabarin da sassafe,

23. da ba su sami jikinsa ba, suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi, sun ga mala'ikun da suka ce yana da rai.

Karanta cikakken babi Luk 24