Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 20:1-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,

2. suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?”

3. Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini,

4. baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?”

5. Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

6. In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.”

7. Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba.

8. Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

9. Sai ya shiga ba jama'a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe.

10. Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi.

11. Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu wofi.

12. Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi.

13. Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’

14. Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’

15. Sai suka jefa shi a bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangijin garkan nan zai yi da su?

16. Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!”

17. Amma ya dube su, ya ce, “Wannan da yake a rubuce fa cewa,‘Dutsen da magina suka ƙi,Shi ne ya zama mafificin dutsen gini?’

18. Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje, amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

19. Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama'a.

20. Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi.

Karanta cikakken babi Luk 20