Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 18:32-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.

33. Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”

34. Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.

35. Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara.

36. Da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko mene ne.

37. Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.”

38. Sai ya ɗaga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

39. Sai waɗanda suke gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

40. Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi,

Karanta cikakken babi Luk 18