Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 18:22-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”

23. Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske.

24. Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!

25. Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

26. Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27. Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”

28. Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.”

29. Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda Mulkin Allah,

30. sa'an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”

31. Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake rubuce kuma game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata.

32. Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.

33. Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”

34. Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.

Karanta cikakken babi Luk 18