Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 2:6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.

7. Amma da suka ga an amince mini in yi wa marasa kaciya bishara, kamar yadda aka amince wa Bitrus ya yi wa masu kaciya bishara,

8. (domin shi da ya yi aiki a zuciyar Bitrus ya sa shi manzo ga masu kaciya, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata, ya sa ni manzo ga al'ummai),

9. sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya.

10. Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.

11. Amma da Kefas ya zo Antakiya, sai na tsaya masa fuska da fuska don laifinsa a fili yake.

12. Don kafin waɗansu su zo daga wurin Yakubu, yakan ci abinci da al'ummai. Amma da suka zo, ya janye jiki ya ware kansa, yana tsoron ɗariƙar masu kaciyar nan.

13. Haka ma sauran Yahudawa masu bi suka nuna fuska biyu kamarsa, ko da Barnaba ma sai da suka ciwo kansa da munafuncinsu.

14. Amma da na ga dai ba sa bin gaskiyar bishara sosai, na ce wa Kefas a gaban idon kowa, “Kai da kake Bayahude, in ka bi al'adar al'ummai ba ta Yahudawa ba, yaya kake tilasta wa al'ummai su bi al'adar Yahudawa?

15. “Mu da aka haifa Yahudawa, ba al'ummai masu zunubi ba,

16. da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a.

17. In kuwa ya zamana, sa'ad da muke neman kuɓuta ga Allah ta wurin Almasihu, an tarar har mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, Almasihu yana hidimar zunubi ne? A'a, ko kusa!

18. Amma in na sāke ginin abin da dā na rushe, na tabbata mai laifi ke nan.

19. Gama ni ta wurin Shari'a matacce ne ga Shari'a domin in rayu ga Allah.

20. An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.

21. Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”

Karanta cikakken babi Gal 2