Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 5:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma wani mutum mai suna Hananiya, da mata tasa Safiratu, ya sayar da wata mallaka tasa,

2. sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin, da sanin matarsa, ya kawo sashin kuɗin kurum ya ajiye a gaban manzanni.

3. Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar?

4. Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.”

5. Da jin wannan magana Hananiya ya fāɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su.

6. Samari suka taso, suka sa shi a likkafani, suka ɗauke shi suka fitar da shi, suka je suka binne shi.

7. Bayan misalin sa'a uku mata tasa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.

8. Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya mini, shin, haka kuka sayar da gonar nan?” Sai ta ce, “I, haka ne.”

9. Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.”

10. Nan tāke, ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka ɗauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta.

11. Sai matsanancin tsoro ya kama dukan Ikkilisiyar, da kuma dukan waɗanda suka ji labarin waɗannan abubuwa.

12. To, an yi mu'ujizai da abubuwan al'ajabi masu yawa a cikin mutane ta hannun manzanni. Dukansu kuwa da nufi ɗaya sukan taru a Shirayin Sulemanu.

13. Amma a cikin sauran mutane ba wanda ya yi ƙarfin halin shiga cikinsu, duk da haka kuwa jama'a suna girmama su.

14. Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama'a masu yawan gaske mata da maza.

15. Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu.

16. Mutane kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da suke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, dukansu kuwa aka warkar da su.

Karanta cikakken babi A.m. 5