Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:21-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Bayan waɗannan al'amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”

22. Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timoti da Arastas, shi kuwa ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.

23. A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan hanya ba.

24. Domin akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin haikalin Artimas da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba yake jawo wa masu yin wannan sana'a ba.

25. Sai ya tara su da duk ma'aikatan irin wannan sana'a, ya ce, “Ya ku jama'a, kun sani fa da sana'ar nan muke arziki.

26. Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.

27. Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”

28. Da suka ji haka suka hasala ƙwarai, suka kuma ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

29. Sai garin duk ya ruɗe, jama'a suka ruga zuwa dandali da nufi ɗaya, suna jan Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus.

30. Bulus ya so shiga taron nan, amma masu bi suka hana shi.

31. Waɗansu zaɓaɓɓun mutanen ƙasar Asiya, waɗanda suke abokansa, su ma suka aika masa, suka roƙe shi kada ya kuskura ya shiga dandalin nan.

32. Taron kuwa, waɗansu suka ta da murya su ce kaza, waɗansu su ce kaza, don duk taron a ruɗe yake, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba.

33. Da Yahudawa suka gabatar da Iskandari, waɗansu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari,

34. amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa'a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

Karanta cikakken babi A.m. 19