Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:19-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama'a duka. Da suka yi wa littattafan nan kima, sai suka ga sun kai kuɗi azurfa dubu hamsin.

20. Sai kuma Maganar Ubangiji ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.

21. Bayan waɗannan al'amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”

22. Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timoti da Arastas, shi kuwa ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.

23. A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan hanya ba.

24. Domin akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin haikalin Artimas da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba yake jawo wa masu yin wannan sana'a ba.

25. Sai ya tara su da duk ma'aikatan irin wannan sana'a, ya ce, “Ya ku jama'a, kun sani fa da sana'ar nan muke arziki.

26. Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.

Karanta cikakken babi A.m. 19