Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 15:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai kuma waɗansu mutane suka zo daga Yahudiya suna koya wa 'yan'uwa, suna cewa, “In ba an yi muku kaciya kamar yadda al'adar Musa take ba, ba dama ku sami ceto.”

2. A kan wannan magana kuwa ba ƙaramar gardama da muhawwara Bulus da Barnaba suka sha yi da mutanen ba. Sai aka sa Bulus da Barnaba da kuma waɗansunsu, su je Urushalima gun manzanni da dattawan Ikkilisiya a kan wannan magana.

3. To, da Ikkilisiya ta raka su, suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tubar al'ummai, sun kuwa ƙayatar da dukan 'yan'uwa ƙwarai.

4. Da suka isa Urushalima, Ikkilisiya, da manzanni, da dattawan Ikkilisiya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu.

5. Amma waɗansu masu ba da gaskiya, 'yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari'ar Musa.”

6. Sai manzannin da dattawan Ikkilisiya suka taru su duba maganar.

7. Bayan an yi ta muhawwara da gaske, Bitrus ya miƙe, ya ce musu, “Ya 'yan'uwa, kun sani tun farkon al'amari, Allah ya yi zaɓe a cikinku, cewa dai ta bakina ne al'ummai za su ji maganar bishara, su ba da gaskiya.

8. Allah kuwa, masanin zuciyar kowa, ya yi musu shaida da ya ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.

9. Bai kuma nuna wani bambanci tsakaninmu da su ba, tun da yake ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyarsu.

10. Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?

11. Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”

12. Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnaba da Bulus, sa'ad da suke ba da labarin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi, da Allah ya yi ga al'ummai ta wurinsu.

13. Bayan sun gama jawabi, Yakubu ya amsa ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, ku saurare ni.

14. Bitrus ya ba da labari yadda Allah ya fara kula da al'ummai, domin ya keɓe wata jama'a daga cikinsu ta zama tasa.

Karanta cikakken babi A.m. 15