Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 3:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.

2. Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.

3. Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.

4. Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne.

5. Kun dai sani an bayyana shi domin yă ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi.

6. Kowa da yake a zaune a cikinsa, ba ya aikata zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.

7. Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne.

8. Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.

9. Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.

10. Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.

11. Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna,

12. kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne.

Karanta cikakken babi 1 Yah 3