Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 2:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ai, ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, ziyartarku da muka yi, ba a banza take ba.

2. Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.

3. Ai, gargaɗin da muke yi muku babu bauɗewa ko munafunci a ciki, balle yaudara,

4. sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu.

5. Yadda kuka sani, ba mu taɓa yin daɗin baki ko kwaɗayi ba. Allah kuwa shi ne shaida.

6. Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga waɗansu, ko da yake da muna so, da mun mori ikon nan namu na manzannin Almasihu.

7. Amma mun nuna taushin hali a cikinku, kamar yadda mai goyo take kula da goyonta.

8. Saboda kuma muna Kaunarku ƙwarai da gaske ne shi ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.

Karanta cikakken babi 1 Tas 2