Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 14:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. A wannan rana ba haske. Masu ba da haske za su dushe.

7. Ubangiji ne ya san wannan rana. Ba rana ba dare. Da maraice ma akwai haske.

8. A wannan rana ruwa mai rai zai gudano daga Urushalima. Rabinsa zai nufi tekun Gishiri, rabi kuma zai nufi Bahar Rum. Zai riƙa malalowa rani da damuna.

9. A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.

10. Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa'an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.

11. Za a zauna cikin Urushalima lami lafiya, ba sauran la'ana.

12. Ga annobar da Ubangiji zai bugi dukan al'ummai da ita, wato su da suka tafi su yi yaƙi da Urushalima. Naman jikunansu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye. Idanunsu kuma za su ruɓe cikin kwarminsu. Harsunansu za su ruɓe a bakunansu.

13. A wannan rana babbar gigicewa daga wurin Ubangiji za ta faɗo musu, har kowa zai kama hannun ɗan'uwansa, ya kai masa dūka.

14. Mutanen Yahuza za su yi yaƙi don su kāre Urushalima. Za a kuma tattara dukan dukiyar al'umman da suke kewaye, su zinariya, da azurfa, da riguna tuli.

15. Annoba irin wannan kuma za ta faɗo wa dawakai da alfadarai, da raƙuma, da jakuna, da dukan dabbobin da suke cikin sansaninsu.

16. Sa'an nan wanda ya ragu daga cikin dukan al'umman da suka kai wa Urushalima yaƙi zai riƙa haurawa zuwa Urushalima kowace shekara, domin yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarkin sujada a lokacin kiyaye Idin Bukkoki.

Karanta cikakken babi Zak 14