Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 72:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa,Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.

8. Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku,Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.

9. Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa,Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.

10. Sarakunan Esbanya da na tsibirai,Za su ba shi kyautai,Sarakunan Arabiya da na HabashaZa su kawo masa kyautai.

11. Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa,Dukan sauran al'umma za su bauta masa!

12. Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi,Da waɗanda suke da bukata,Da waɗanda ba a kula da su.

13. Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta,Yakan ceci rayukan waɗanda suke da bukata.

14. Yakan cece su daga zalunci da kama-karya,Rayukansu suna da daraja a gare shi.

15. Ran sarki yă daɗe!Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya,Da ma a yi masa addu'a dukan lokaci,Allah ya sa masa albarka kullum!

16. Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar,Da ma amfanin gona yă cika tuddan,Yă yi yawa kamar itatuwan al'ul na Lebanon,Da ma birane su cika da mutane,Kamar ciyayin da suke girma a sauruka.

Karanta cikakken babi Zab 72